Home Labaru Zaben 2023: INEC Ta Yi Wa Mutane Miliyan 1.9 Rajista Ta Yanar...

Zaben 2023: INEC Ta Yi Wa Mutane Miliyan 1.9 Rajista Ta Yanar Gizo

46
0
Rajistan Takin Zabe

Hukumar Zaɓe mai zaman kan ta ta Ƙasa INEC, ta samu buƙatar yin rajista miliyan 2 da dubu 449 da 648 daga ranar da ta fara aikin rajistar masu zaɓe kamar yadda jadawalin mako-mako na aikin ya nuna.

Jadawalin ya kuma nuna cewa, ya zuwa yanzu ‘yan Nijeriya miliyan 1 da dubu 923 da 725 ne su ka kammala matakan farko na yin rajistar su ta hanyar yanar gizo.

 Hukumar, ta ce ‘yan Nijeriya dubu 315 da 791 ne su ka kammala rajistar su ta hanyar yanar gizo ko ta hanyar ido da ido a cibiyoyin yin rajista da ke faɗin ƙasar nan a wannan tsakani.

Ta ce buƙatun yin rajista miliyan 2 da dubu 449 da 64 da ta karɓa sun haɗa da masu son yin sauyin wurin zaɓe da masu son a sauya masu katin zaɓe da masu son a gyara masu bayanan su da ke kan katin su na zaɓe, da sauran su.