Home Labaru Ci-Gaban Kasa: Atiku Abubakar Ya Koka Game Da Lamarin Yawaitar Ta’Addanci

Ci-Gaban Kasa: Atiku Abubakar Ya Koka Game Da Lamarin Yawaitar Ta’Addanci

44
0
Atiku-Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya yi Allah-Wadai da yawaitar fashi da makami a fadin Nijeriya.

Atiku Abubakar, ya ce ba zai zama abin mamaki ba idan ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane sun nemi yin rajista da Hukumar Kula da Harkokin Kamfanoni da neman sunayen a jerin Kasuwar Hannayen Jari ta Nijeriya.

Ya ce dole ne a sake fasalin Nijeriya domin a samu gagarumin ci-gaba cikin hanzari, ya na mai cewa akwai bukatar gyara Nijeriya domin guje wa afkawa cikin bala’i.

Atiku Abubakar ya bayyana haka ne, a wajen tattaunawar kasa tare da gabatar da wani littafi mai taken, “Sake gyara Nijeriya’, inda ya ce sake fasalin Nijeriya ya zama dole don ganin an samu ci-gaba mai dorewa.