Home Labaru Wata Sabuwa: Za A Fara Kama Mabarata Da Masu Talla A Jihar...

Wata Sabuwa: Za A Fara Kama Mabarata Da Masu Talla A Jihar Legas

197
0
Mabarat A Legas

Gwamnatin Jihar Legas ta haramta bara a kan titina, sannan ta kafa hukuma ta musamman domin dakatar da barace-barace, wadda ake sa ran za ta fara aiki a cikin ‘yan kwanakin masu zuwa.

Wani jami’in jihar da ke kula da ci-gaban matasa Olusegun Dawodu ya shaida wa manema labarai cewa, mabarata a kan tituna su na cutar da ‘yan kasa masu bin doka.

Olusegun Dawodu, ya ce ana yin safarar mabarata da masu talla da su ka hada da kananan yara daga wasu sassan Nijeriya zuwa birnin Lagos.

Ya ce kasuwancin ya na kaskantar da kai tare da sa a ci zarafin bil-Adama, musamman kananan yaran da aka tilasta wa shiga barace-barace.

Dawodu ya kara da cewa, wasu daga cikin mabarata da masu saida kaya a kan titi su na da alaka da aikata laifuffuka a cikin gari ta hanyar kai hari da fashi ga mazauna birnin.

Ya ce ayyukan mutanen su na janyo koma-bayan ga zirga-zirgar mutane da ababen hawa, sannan ya na haifar da illa ga muhalli da barazanar tsaro.

Leave a Reply