Home Labaru Zaben 2023: Gwamnonin Arewa Sunyi Watsi Da Tsarin Karba-Karba

Zaben 2023: Gwamnonin Arewa Sunyi Watsi Da Tsarin Karba-Karba

99
0

Gwamnonin Arewacin Najeriya 19 sun bayyana tsarin karba-karba a kujerar Shugaban Kasa a matsayin abin da ba ya cikin Kundin Tsarin Mulki.

Sun bayyana hakan ne a karshen taron da suka gudanar ranar Litinin a Kaduna, yayin da suke mayar da martani ga takwarorinsu na Kudu wadanda suka tsaya kai da fata cewa dole Shugaban Kasa mai zuwa ya fito daga yankinsu.
A wani taro da suka gudanar a Legas a kwanakin baya, Gwamnonin Kudun sun bukaci dole mulki ya koma yankinsu idan Shugaba Muhammadu Buhari ya kammala wa’adinsa a 2023.
To sai dai a karshen taronsu na Kaduna, Gwamnonin na Arewa sun ce ko da yake akwai wasu daga cikinsu da suka nuna goyon bayan mulkin ya koma Kudu don amfanin hadin kan kasa, matsayin da takwarorin nasu na Kudu suka dauka ba abu ba ne da za su lamunta.
Da yake karanta matsayinsu, Shugaban Gwamnonin, kuma Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong ya ce, “Matsayin da suka dauka ya ci karo da tanadin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima.
Ko baya ga karba-karba Kungiyar gwamnonin arewan tattauna kan matsalar tsaron da ya addabi yankin.