Home Labaru Zaben Magajin Merkel: Jamusawa Sun Kada Kuri’a

Zaben Magajin Merkel: Jamusawa Sun Kada Kuri’a

14
0

Miliyoyin Jamusawa sun jefa kuri’a a zaben Jamus da ke kawo karshen shugabancin gwamnatin kasar da Angela Merkel ta shafe shekaru da dama tana yi.

Zaben dai shi ne irin sa na farko tun lokacin da gabashi da kuma yammacin Jamus suka sake hadewa a shekarar 1990, wanda kuma shugabar gwamnatin kasar mai barin gado Angela Merkel ba za ta shiga takara ba, bayan shafe shekaru 16 kan mukamin na ta.

Sakamakon wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka yi ana dab da zaben na Jamus, ya nuna cewar har yanzu jam’iyyar Social Democrat ta SPD ke kan gaba wajen karbuwa, fiye da jam’iyyar Merkel ta Christian Democratic Union CDU da kuma wadda suke kawance ta Christian Social Union CSU.

Kuri’ar jin ra’ayin jama’ar ta baya bayan nan ta sanya  zaben shugabancin gwamnatin ta Jamus zama mai zafi tsakanin bangaren masu hammaya da masu mulki.