Home Labaru Ce-Ce-Ku-Ce: Gwamnan Adamawa Ya Bayyana Dalilan Da Yasa Zasu Ciwo Bashin Naira...

Ce-Ce-Ku-Ce: Gwamnan Adamawa Ya Bayyana Dalilan Da Yasa Zasu Ciwo Bashin Naira Biliyan 100

108
0

Ana ci gaba da ce-ce-ku-ce kan shirin gwamnatin jihar Adamawa na karbo rancen naira biliyan 100.
Gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri ya ce za a yi amfani da kudin ne wajen gyara kasuwannin dabbobi da kuma hatsi don inganta samun kudin shiga a jihar.

A wata hira da BBC, Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya ce ya zama dole a samo sabbin hanyoyin samun kudin shiga domin rage dogaro kan gwamnatin tarayya da kuma kudin mai.
To amma ita kuwa jam’iyar APC mai adawa ta ce dabara ce ta wawure kudin al’umma.
Tun a lokacin da gwamnan ya sanar da cewa gwamnatinsa za ta karbi rancen a watan Mayu ne aka fara tayar da jijiyoyin wuya tsakanin bangaren gwamnati da na ‘yan adawa a jihar.
Gwamna Fintiri ya ce ‘yan adawa ne ba su fahimci yadda abin yake ba.

Leave a Reply