
Jam’iyyar APC ta yi fatali da sukar da wasu ke yi cewa shugaba Muhammadu Buhari na janye jiki daga tafiye-tafiyen da ake yi na yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam`iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu.
Jam’iyyar ta ce a matsayin sa na shugaban kasa bai dace ya jingine aikin sa na jagorancin al’ummar Najeriya saboda yakin neman zabe ba.
A tattaunawar da ya yi da BBC, shugaban jam’iyyar APC na kasa Sanata Abdullahi Adamu ya ce sun gamsu da yakin neman zaben, kuma ba sa shakkar abokan hamayyar su.
Ya ce mutane sun riga sun karbi sakon jam’iyar APC, kuma dukkan sauran jam’iyyu sun san ana gaban su.
Kan ikirarin shugaban kasa Buhari na janye jiki daga tarukan jam’iyyar, Abdullahi Adamu ya ce babu kanshin gaskiya kan batun.
Ya ce Buhari yafi kowa son APPC ta yi nasara.













































