Home Home Ci Da Addini: El-Rufai Ya Ce  Lokaci Ya Yi Da Za A Hukunta...

Ci Da Addini: El-Rufai Ya Ce  Lokaci Ya Yi Da Za A Hukunta ‘Yan Siyasa Masu Amfani Da Addini

131
0
Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai, ya ce lokaci ya yi da za a cire batun addini daga siyasar ƙasa tare da hukunta ‘yan siyasar da ke amfani da addini a matsayin makamin yaƙin neman zaɓe.

Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai, ya ce lokaci ya yi da za a cire batun addini daga siyasar ƙasa tare da hukunta ‘yan siyasar da ke amfani da addini a matsayin makamin yaƙin neman zaɓe.

Gwaman El-rufa’i, ya bayyana haka ne a ranar Talata a lokacin bikin ƙaddamar da babban ofishin ‘gidauniyar zaman lafiya da ci gaba’ ta mai alfarma sarkin musulmi.

El-Rufai ya yi kira ga Sarakunan gargajiya da malaman addini su riƙa gudanar da addu’o’in samun ingantaccen zaɓe da samun zaman lafiya a fadin Najeriya.

Ya ce a matsayin sa na ɗan ƙasa, kuma gwamna sannan kuma musulmi baya jin daɗin yadda wasu ‘yan siyasa ke amfani da addini da ƙabilanci a matsayin makamin su na yaƙin neman zaɓe.

Haka kuma gwamnan ya ce lokaci ya yi da za a cire batun addini daga siyasar ƙasa tare da hukunta waɗanda ke ƙoƙarin amfani da addinin a matsayin makamin yaƙin neman zabe.

Leave a Reply