Home Labaru Zaben 2019: Omo Agege Ya Ce Babu Ba Za A Taba Da...

Zaben 2019: Omo Agege Ya Ce Babu Ba Za A Taba Da Na Sanin Sake Zabar Buhari Ba

321
0

Mataimakin Shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo Agege ya ce babu dan Najeriya da zai yi da na sanin sake zaben Shugaba Muhammadu Buhari a karo na biyu.

Omo Agege, ya bayyana haka ne a mahaifar sa ta Orogun dake karamar hukumar Ughelli ta arewa a Jihar Delta a lokacin da ake lale murhabun da ziyarar da ya kai kauyen.

Ya ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari, na da manufar kawo gyara a Najeriya domin kasancewar sa mataimakin Shugaban majalisar dattawa na da nasaba da sa hannun Shugaba Buhari da kuma wasu jiga-jigan jam’iyyar APC.  

Tun bayan da aka zabe Omo Agege dake wakiltar Delta ta tsakiya a majalisar dattawa a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattawa, wannan ne karo na farko da ya ziyarci kauyen nasa.

Omo-Agege ya ce wannan matsayi na mataimakin shugaban majalisar dattawa, yankin su na kudu maso kudu bai taba samu ba tun shekarar 1999 sai ga shi goyon bayan Shugaba Buhari ya kai su ga wannan nasara. AnN��JI&