Home Labaru Garkuwa Da Mutane: ‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Wasu Manyan...

Garkuwa Da Mutane: ‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Wasu Manyan Fastoci A Ogun

240
0

Wasu gungun ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da wasu manyan Limaman cocin ‘Redeemed Christian Church of God’ RCCG a jahar Ogun kamar yadda rahotanni su ka bayyana.

Shugaban cocin Fasto Adeboye

Shugaban cocin Fasto Adeboye ya bayyana haka, inda ya ce ‘yan bindigar sun yi garkuwa da Fastocin ne yayin da su ke kan hanyar zuwa Legas domin halartar wani babban taron cocin.

A cewar sa, an kama fastocin ne a kan babbar hanyar Ije-Ode, don haka ya yi kira ga ‘yan cocin su dage da addu’a domin ganin Fastocin sun kubuta daga hannun ‘yan bindigar.

Fasto Adeboye ya cigaba da cewa, wannan ne karo na farko da irin wannan ta faru ga Fastocin cocin su.