Home Labaru Matsalar Tsaro: Obasanjo Ya Gana Da Shugabannin Kungiyar Fulani

Matsalar Tsaro: Obasanjo Ya Gana Da Shugabannin Kungiyar Fulani

532
0

Kungiyar Fulani makiyaya ta Gan Allah Fulbe wato GAFDAN,  ta yi wani taro da tsohon shugaban Kasa Olusegun Obasanjo a Abeokuta babban birnin jihar Ogun

Taron na da alaka da matsalar tsaro da halin da Fulani makiyaya ke ciki inda ake alakant a su da aikata miyagun laifuka da suka  hada yin garkuwa da mutane da aikata wasu laifuka a yankunan Kudu maso Yamma.

Taro Da Tsohon shugaban kasa Obasanjo da shugabanin fulani

A cikin wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban kungiyar Fulani ta GAFDAN na kasa, Sale Bayari, da sauran wakilan kungiyoyin Fulani daga Kudu maso Yamma da wakilan jihohin Kogi da Kwara.

Sauran sun hada da mai Magana da yawun kungiyar Yarbawa zalla ta Afenifere, Yinka Odumakin da  Dayo Adewole, dan tsohon Ministan lafiya Farfesa Isaac Adewole, wanda aka yi garkuwa da shi a Oyo aka kuma sako shi ba da jimawa ba.agram N��\I

Leave a Reply