Home Labaru Zaben 2019: INEC Ta Kwace Shahadar ‘Yan Takara 25 Bisa Umarnin Kotu

Zaben 2019: INEC Ta Kwace Shahadar ‘Yan Takara 25 Bisa Umarnin Kotu

312
0
Hukumar Zabe Mai Zaman Kan Ta kasa, INEC
Hukumar Zabe Mai Zaman Kan Ta kasa, INEC

Hukumar Zabe Mai Zaman Kan ta ta Kasa INEC, ta bayyana kwace shahadar lashen zaben ‘yan takara 25 aka bayyana sun yi nasara a baya, bayan wasu da su ka kai kararraki a kotuna sun yi nasara.

Babban Jami’in hukumar zabe Festus Okoye ya bayyana haka, yayin da ya ke jawabi a wajen taron da Kungiyar ‘Yan Jaridu ta Kasa ta shirya a Enugu.

Kungiyar ‘yan jaridar dai ta shirya taron ne, domin tattauna rawar da hukumar zabe ta taka a zabubbukan shekara ta 2019 da ta gudanar.

Okoye, ya jinjina wa kafafen yada labarai bisa gagarumar rawar da su ka taka kafin zabe, da lokacin gudanar da zabe da kuma bayan kammala shi. Ya ce kafafen yada labarai ne daukacin talakawa su ka rika dogara da su, domin samun bayanan yadda zabubbuka ke gudana, sannan ita kan ta hukumar zabe da su ta rika amfani domin isar da sakonnin ta ga jama’a.