Home Labaru Kalaman Obasanjo: Fadar Shugaban Kasa Ta Maida Kakkausan Martani

Kalaman Obasanjo: Fadar Shugaban Kasa Ta Maida Kakkausan Martani

376
0
Obasanjo, Tsohon Shugaban Kasa
Obasanjo, Tsohon Shugaban Kasa

Gwamnatin tarayya, ta ce kalaman da tsohon shugaban kasa Obasanjo ya yi a kan yakin da gwamnati ke yi da Boko Haram na iya janyo rabuwar kai tsakanin mabiya addinai da mabambanta kabila a Nijeriya.

Idan dai ba a manta ba, Obasanjo ya ce kungiyopyin Boko Haram da ISWAP su na kokarin musuluntar da Nijeriya ne ko Afirka ta Yamma.

Gwamnatin tarayya, ta ce kalaman su na da matukar muni, kuma abin kunya ne a rika samun dattajo kamar Obasanjo ya na furta irin wadannan kalamai.

Ministan yada labarai Lai Mohammed, ya ce tun lokacin da rikicin Boko Haram ya shigo, ‘yan ta’addan sun fi kashe musulmi tare da lalata masallatai fiye da mabiya wasu addinai. A karshe Ministan ya shawarci Obasanjo da cewa, kada ya bari gabar da ke tsakanin sa da Shugaba Buhari ta sha karfin kaunar da ya ke yi wa Nijeriya.

Leave a Reply