Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya gana da wakilan al’ummar Nijeriya mazauna kasar Saudiyya.
Yayin takaitacciyar ganawar, wakilan ‘yan Nijeriya da ke zaune a kasar Saudiyya, sun sanar da shugaba Buhari irin ayyukan da kungiyar su ke yi a kasa mai tsarki.
Jim kadan bayan kammala ganawar ne, shugaba Buhari ya tashi daga filin jirgin sama na kasa da kasa na sarki Abdul’aziz da ke Jeddah. Idan dai ba a manta ba, rahotanni sun ce shugaba Buhari ya sha ruwa tare da jagoran jam’iyyar APC na kasa Bola Tinubu, da mai alfarma sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III, da wasu manyan ‘yan Nijeriya a kasar Saudiyya.
You must log in to post a comment.