Home Labaru Zaben 2019 : Ganduje Ya Gabatar Da Shaida

Zaben 2019 : Ganduje Ya Gabatar Da Shaida

621
0

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya fara kare kansa a gaban kotun sauraron karar zaben jihar, inda ya gabatar da shaidan baka da wasu takardu, sai dai an gano shaidan ya na dauke da katin zabe ne na bogi.

Idan ba a manta ba kotun sauraron karar da jam’iyyar PDP da dan takarar gwamnan ta Abba Kabir Yusuf, suka shigar ne na kallubalantar nasarar Ganduje a zaben gwamna da aka gudanar a watan Maris din 2019.

Wadanda aka yi karar sun kuma gabatar da shaidun bakuna uku daga mazabar Gama dake karamar hukumar Nasarawa a jihar.

Shaidan na farko, Abubakar Suleiman, daga mazabar Gama ya yi ikirarin cewa a zaben ranar 9 ga watan Maris, wasu magoya bayan PDP a akwatin zaben sa, sun mika sunayen wasu mutane 20 ga jami’an INEC kuma suka hakikance dole sai sun fara yin zabe kafin wani ya jefa. Sai dai abin mamaki a lokacin da aka bukaci Suleiman ya gabatar da katin zaben sa, sai aka gano katin na dauke da sunan Sadiq Sadiq, hakan ya sa lauyan PDP Eyitayo Fatogun tafka mahawara mai zafi da lauyan Ganduje