Gwamnatin tarayya ta ce ta fara shirye-shiryen daukan matasa masu yi wa kasa hidima marasa aiki, a shirin samar da aiki na N-Power.

Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki ne, ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru bayan kammala taron majalisar tattalin arzikin kasa daya gudana a fadar gwamnati da ke Abuja.
Taron ya gudana ne a karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya je Zariya dake jihar Kaduna domin kaddamar da wasu manyan ayyuka.
Gwamnan ya ce gwamnati na duba yiwuwar daukan matasa, masu yi wa kasa hidima da kuma na N-Power aikin a karkashin dokar da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, za ta kaddamar mai suna Community Policing.
You must log in to post a comment.