Home Labaru Aikin ‘Dan Sanda: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Sanar Da Dalibai

Aikin ‘Dan Sanda: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Sanar Da Dalibai

756
0

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta sanar da daliban da suka nemi samun gurbin karatu a makarantar horar da ‘yan sanda ta Wudil dake Kano, cewa za a rubuta jarabawar sabbin shiga a ranar Asabar 24 ga watan Agusta.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas Bala Elkana,

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas Bala Elkana, ne ya bada wannan sanarwar inda ya ce cibiyoyin rubuta jarabawar a Legas sun hada da Kwalejin ‘yan sanda ta Ikeja, da Kings College da Makarantar mata ta Anwarul Islam.

Bala Elkana ya ce rundunar ta bayar da sanarwan cewar kowa ya fitar da katin sa na jarabawar a yanar gizo kuma dole ne mutum ya kasance a wurin rubuta jarabawar da karfe 7 na safiya daidai, na ranar jarabawar.