Home Coronavirus Za Mu Wadatar Da Riga-Kafin Covid-19 Kasashen Duniya – China

Za Mu Wadatar Da Riga-Kafin Covid-19 Kasashen Duniya – China

639
0
Za Mu Wadatar Da Riga-Kafin Covid-19 Kasashen Duniya - China
Za Mu Wadatar Da Riga-Kafin Covid-19 Kasashen Duniya - China

Gwamnatin kasar China ta ce zata sakin riga-kafin cutar coronavirus domin amfanin al’ummar duniya da zarar ta kammala gwajin riga-kafin a dakunan na binciken ta.

Shugaban China Xi Jinping ya bayyana haka a yayin gabatar da jawabi a zauren Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya.

Yanzu haka dai, kasar China na da nau’ukan riga-kafin cutar coronavirus guda biyar da ake gwajin su a dakin binciken kimiyar ta, a dai-dai lokacin da kasashen duniya ke rige-rigen dakatar da kwayar cutar, wadda ta kashe sama da mutane dubu 316 a sassan duniya.

Shugaba Xi ya ce, samar da riga-kafin annobar, zai kasance gudunmawar China ga kasashe masu tasowa da ake ganin za su samu riga-kafin cikin sauki.

Xi Jinping ya kuma shaida wa zauren Hukumar Lafiyar ta Duniyar cewa, kasar sa za ta bada tallafin dala biliyan 2 domin yaki da COVID-19 a cikin shekaru biyu.