Hukumar Lafiya ta Duniya ta fara gudanar da taron ta na shekara-shekara wanda ta ke ba masana harkokin kula da lafiya da shugabannin kasashe damar tattaunawa a kan batutuwan da suka shafi kiwon lafiya da kuma annobar da ake samu.
Taron na bana dai, na zuwa ne a dai-dai lokacin da duniya ke fama da annobar COVID-19, yayin da kasashen Amurka da China ke takun saka kan batun bayanan cutar, matsalar da ta shafi Hukumar lafiya ta duniya WHO.
WHO ta ce taron wanda aka saba kwashe makwanni 3 ana gudanar da shi, amma a wannan karon za a dauki kwana biyu ne kacal, saboda annobar COVID-19 wadda ta kashe mutane sama da dubu 310, ta kuma hana zirga-zirgaa sassan duniya.
Barkewar cutar COVID-19 da kuma yadda kasashen duniya suka tinkari matsalar, da kuma batun samun maganin rigakafi da kuma rarraba shi ake saran zai mamaye taron, yayin da masana kimiya ke aikin tukuru domin ganin sun samu nasara.