Home Labaru Ilimi Za Mu Janye Malamai Daga Yankunan Da Babu Tsaro – NUT

Za Mu Janye Malamai Daga Yankunan Da Babu Tsaro – NUT

133
0

Kungiyar malamai ta kasa NUT, ta koka da yadda rashin tsaro  ke kara ta’azzara a kasar nan, inda ta ce ta rasa malamai 800 a yankin arewacin Nijeriya.

Haka kuma, kungiyar ta yi barazanar janye malaman ta daga wasu kananan hukumomi da ke yankin arewa maso yamma, saboda ta’azzarar matsalar garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’addanci.

Shugaban kungiyar Dr Nasir Idris ya bayyana haka, yayin wata tattaunawa da manema labarai a Abuja, inda ya ce aikin gwamnatin tarayya ne kulawa da rayuka da dukiyoyin jama’ar kasar nan.

Dr Idris, ya ce  yankin arewa maso gabashin Nijeriya sun rasa malamai 800, yayin da aka yi garkuwa da wasu malamai mu da yaran su a yankin arewa maso yamma, saboda wasu malaman sun nuna cewa ba za su yarda a saci dalibai a bar su ba.

Ya ce duk yankin da gwamnatin tarayya ta kasa samar da isasshen tsaro, za su bukaci malamai su janye su hakura da aikin.

Leave a Reply