Wata kotun majistire da ke zama a Kano, ta haramta wa mutumin da ake zargi da yi wa gwamna Abdullahi Umar Ganduje batanci rubutu a dandalin msada zumunta na Facebook.
Kotun dai ta ɗauki matakin ne, domin ci-gaba da sauraren shari’ar, yayin da Alkalin kotun Mai shari’a Aminu Gabari ya janye belin da ya ba wanda ake zargin Muazu Magaji Danbala kiru.
Alkalin kotun ya ɗauki matakin janye belin ne, biyo bayan gaza cika sharuɗɗan da aka gindaya ma wanda ake tuhuma, kuma lauyan sa ya nuna cewa sharuɗɗan sun yi tsauri.
Shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa Auwalu Aramfo ne ya kai karar mutunanen biyu, wadanda su ka hada da Muazu Magaji Danbala da kuma Jamilu Shehu.