Home Labaru Kotu Ta Yanke Wa Maina Hukuncin Shekaru 8 A Gidan Yari

Kotu Ta Yanke Wa Maina Hukuncin Shekaru 8 A Gidan Yari

68
0

Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta kama tsohon shugaban hukumar fansho ta kasa Abdulrasheed Maina da laifin sata da kuma halasta kudin haram.

A wani hukunci da mai shari’a Okong Abang ya yanke, ya ce kotun ta kama Maina da laifin satar kudi sama da naira biliyan biyu na ‘yan fansho, wadanda da yawan su sun rasu kuma ba su ci moriyar hakkokin sub a.

Alkalin ya kara da cewa, ya yanke wa Abdulrasheed Maina hukuncin daurin shekaru takwas a gidan yari.

Idan dai ba a manta ba, a baya kotu ta daure Faisal Maina, wanda ta kama da laifuka uku, wadanda su ka hada da halasta kudin haram har Naira Miliyan 58 da dubu 100, sai dai har yanzu babu rahoton cewa Faisal ya na gidan yari.