Ministan harkokin ‘yan sanda Mohammed Maigari Dingyadi, ya ce Ibrahim Magu zai gurfana a gaban kotu ne kawai idan an kai rahoton binciken da ake gudanarwa a kan shi, wanda mai shari’a Ayo Salami ke jagoranta.
Maigari Dingyadi ya bayyana haka ne, a wajen taron ministoci na mako-mako da tawagar yada labarai ta shugabancin Nijeriya a Abuja.
Idan dai ba a manta ba, a watan Yuli na shekara ta 2020 ne, shugaba Buhari ya kafa kwamitin da za ta gudanar da bincike a kan zarge-zargen da ake yi wa Magu, biyo bayan koken da Babban Lauyan Gwamnatin tarayya Abubakar Malami ya shigar.
An dai kafa kwamitin ne a ƙarƙashin shugabancin mai shari’a Ayo Salami, wadda tun bayan kammala binciken ya miƙa rahoton shi ga Shugaba Muhammadu Buhari.