Home Labarai Boko Haram Da Ta’ammali Da Muggan Kwayoyi Ya Yi Tsanani A Jihar Kaduna...

Boko Haram Da Ta’ammali Da Muggan Kwayoyi Ya Yi Tsanani A Jihar Kaduna – El-Rufai

76
0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i, ya gargadi jami’an tsaro su kara maida hankali, domin alamu sun nuna cewa kungiyoyin Boko Haram da Ansaru sun shigo jihar Kaduna.


El-Rufa’i, ya ce muddin ba a maida hankali wajen kawo karshen wannan matsalar ba tunda wuri, za a shiga matsanancin halin rashin tsaro a yankin Arewa Maso Yamma, fiye da wanda aka yi fama da shi a yankin Arewa Maso Gabas saboda akwai karancin jami’an tsaro da ake fama da shi.


Gwamna El-Rufa’i ya bayyana haka ne, a lokacin da ya ke jawabi a wajen mika rahoton bayanai a kan tsaron jihar Kaduna na wata-wata da ma’aikatar tsaro ta jihar ta yi.


Ya ce baya ga kwararowar Boko Haram jihar Kaduna, yanzu haka sun mamaye yankunan kananan hukumomin birnin Gwari da Chikun, an kuma samu yawaitar dashe- dashen nakiyoyi a sassan jihar da dama.


A karshe ya yaba wa jami’an tsaro bisa kokarin da su ke yi wajen ganin ana samun nasara a harkar tsaron jihar Kaduna, yayin da ya ce jami’an sa-kai da gwamnati ta dauka su na taimakawa wajen harkar tsaro.