Home Labaru Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Sace Dan Majalisar Jihar Anambara

Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Sace Dan Majalisar Jihar Anambara

350
0

A Najeriya, ‘yan bindiga a jihar Anambra sun sace dan majalisar dokokin jihar mai wakiltar mazabar gwamnan jihar Charles Soludo.

 ‘Yan sandan jihar sun tabbatar da sace  Okechukwu Okoye, wanda yake wakiltar mazabar Aguata ta 1 a majalisar dokokin jihar Anambra.

Mr Okoye,  wanda dan asalin kauyen Usofia, inda nan ne mahaifar Charles Soludo, gwamnan jihar Anambra, ya shiga hannun ‘yan bindigar ne a ranar Lahadi.

Kakakin ‘yan sandan jihar ta Anambra, Toochukwu Ikenga, ya tabbatar wa da kamfanin dillacin labaran Najeriya aukuwar lamari, inda yace an gano motar Jeep, wadda dan majalisar yake cikinta a lokacin da aka sace shi.

Mr Ikenga ya ce ‘yan sanda sun kaddamar da farautar wadannan ‘yan bindiga da zummar ceto wanda aka yi garkuwa da shi.

Leave a Reply