Home Home Gwamnatin Najeriya Ta Ce Ba Za Ta Iya Ci Gaba Da Biyan...

Gwamnatin Najeriya Ta Ce Ba Za Ta Iya Ci Gaba Da Biyan Tallafin Lantarki Ba

241
0

Ministan lantarki Adebayo Adelabu ya ce Nijeriya ba za ta iya ci gaba da biyan kuɗin tallafin wutar lantarki ba.

Adelabu ya ce dole ne Nijeriya ta fara ɗaukar mataki domin magance basukan da kamfanonin samar da wutar lantarki ke bin gwamnati.

Ya ce yanzu bashin da kamfanonin ke bin gwamnatin tarayya ya kai Naira tiriliyan 1 da biliyan 300, sannan wanda kamfanonin samar da gas ke bi sun kai Naira biliyan 1 da miliyan 300.

Adelabu ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudana a Abuja, sannan ya ce kasafin kuɗin shekara ta 2024 ya ware Naira biliyan 450 domin biyan tallafin, yayin da ma’aikatar lantarkin ke buƙatar fiye da Naira tiriliyan biyu domin biyan tallafin.

Haka kuma, Adelabu ya ce yanzu haka za a ba gwamnatocin jihohi damar samar da wutar kansu domin raba wa jihohinsu, sannan ya ce kamfanin samar da wutar na Nijeriya ya jingine fiye ayyukansa 100, saboda samun ƙari a kuɗaɗen kwangilolin ayyukan sakamakon tashin farashin dala. Mista Adelabu ya cigaba da cewa, an kuma ware fiye da Naira biliyan 50 a kasafin 2024, domin gina ƙananan tasoshin samar da wutar lantarki a yankunan karkara.

Leave a Reply