Home Labaru Za Mu Ajiye Bambancin Mu Yi Wa Nijeriya Aiki – Ahmad Lawan

Za Mu Ajiye Bambancin Mu Yi Wa Nijeriya Aiki – Ahmad Lawan

650
0
Sanata Ahmed Lawan, Shugaban Majalisar Dattawa
Sanata Ahmed Lawan, Shugaban Majalisar Dattawa

Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan, ya ce lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya za su yi watsi da bambance-bambancen siyasa su yi wa kasar su aiki.

Karanta Wannan: Zamfara: ‘Yan Bindiga, ‘Yan Sintiri Za Su Yi Sulhu

Sanatan ya nuna cewa, majalisa ta na neman hanyar da ‘ya‘yan ta za su rabu da duk wata akidar siyasar su don ganin an yi abin da zai kai Nijeriya gaci.

Shugaban majalisar dattawan ya bayyana haka ne, yayin da ya halarci wani taro da Sanata Sani Musa daga jihar Neja ya shirya domin tattaunawa da mutanen Mazabar sa.

Sanata Ahmed Lawan ya kara da cewa, sun kama hanyar nuna wa Duniya yadda hukumomin Nijeriya za su hadu su yi aiki da juna ba tare nuna bambancin siyasa ba.