Home Labaru Babban Burin Mu Shi Ne Samar Da Ayyukan Yi – Buhari

Babban Burin Mu Shi Ne Samar Da Ayyukan Yi – Buhari

469
0
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya jadadda cewa kudurin gwamnatin sa a yanzu shi ne samar da guraben ayyukan yi.

Karata Wannan: Siyasar Kano: Kotu Ta Tabbatar Da Takarar Abba Kabir Yusuf Na Jam’iyyar PDP

A cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai Femi Adesina ya fitar, ya ce Gwamnatin Tarayya ta nuna haka ne ta hanyar zuba kudi a fannin noma, da ma’aikatar hakar ma’addinai da hukumomin samar da ayyuka a shekaru hudu da su ka gabata.

Adesina, ya ce shugaba Buhari ya yi korafin cewa, rufe masaku musamman a yankin Arewacin Nijeriya ya yi sanadiyyar haifar da yawaitar miyagun laifuffuka.

Yayin da ya ke tuni game da umurnin sa ga dukkan cibiyoyin gwamnati masu samar da kayan sarki da su taimaka wajen sayen kayan daga kamfanonin kasa, Shugaba Buhari ya ce za a samar da yawancin ayyuka idan rundunar soji ‘yan sanda da hukumomin tsaro da hukumar bautar kasa su ka soma sayen kayan kamfanonin gida.

A karshe  ya nuna takaicin rashin masakun kayan sawa da ke samar da miliyoyin ayyuka sama da Gwamnatin Tarayya a zamanin baya.