Home Labaru ‘Yan Nijeriya Sun Fara Tsokaci A Kan Stawagar Ministocin Buhari

‘Yan Nijeriya Sun Fara Tsokaci A Kan Stawagar Ministocin Buhari

289
0
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

‘Yan Nijeriya sun fara maida martani a kan sunayen mutanen da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar wa majalisa domin tantance su a matsayin ministocin sa.

Karanta Wannan: Kisan Kai: Kotu Ta Yi Wa Wanda Ya Kashe Marasa Lafiya 85 Daurin Rai-Da-Rai A Jamus

A jerin sunayen dai babu akasarin ministocin da su ka yi aiki a wa’adin mulki na farko, yayin da wasu sabbin mutane su ka samu shiga.

Sai dai batun rashin ba matasa gurabe sosai da kuma mata ya dauki hankalin wasu daga cikin masu bibiyar al’amurran siyasar Nijeriya.

Da yak e tsokaci a kan lamarin, Dakta Aliyu Tilde ya ce babu laifi a tawagar da shugaba Buhari ya mika wa majalisa, duk da cewa an sa ran dawowar wasu tsofaffin ministocin da sunayen su su ka sake bayyana.

Sai dai a nata bangaren, jam’iyyar PDP ta bayyana jerin sunayen ministocin a matsayin tawagar da ke cike da mutanen da su ka gaza sauke nauyin da aka taba dora masu a baya.

Mai Magana da yawun jam’iyyar PDP Kola Ologbondiyan, ya ce babu kwarin gwiwa tattare da sabuwar tawagar ministocin dangane da fatan magance kalubalen da Nijeriya ke fuskanta.