Home Labaru Za A Hukunta Masu Gine-Ginen Da Basu Kammala Ba A Abuja

Za A Hukunta Masu Gine-Ginen Da Basu Kammala Ba A Abuja

42
0

Hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja (FCTA) ta ce ta shirya tsaf don hukunta masu gidajen da suka ƙi kammala ginin su a ƙwaryar birnin.

Wata sanarwa da daraktan filaye Alhaji Adamu Hussaini ya fitar wadda kuma jaridar Daily Trust ta ruwaito ta ce sun ɗauki matakin ne domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin mazauna Abuja mai girman murabba’in kilomita 250.

Yace domin tabbatar da tsaron lafiyar rayuka da dukiyoyi a ciki da kewayen murabba’in kilomita 250 na Abuja, akwai yiwuwar hukumar ta kamamala shirye-shirye domin hukunta masu gidajen da suka bar su ba tare da an kammala ba,” a cewar sanarwar.

Ya ƙara da cewa hukuncin za su haɗa da ƙwace shaidar mallaka, sannan ya shawarci masu gidajen da su kammala ginin su.