Home Labaru Korona Ta Sake Kashe Mutum Biyu 859 Sun Kamu A Najeriya Ranar...

Korona Ta Sake Kashe Mutum Biyu 859 Sun Kamu A Najeriya Ranar Litinin

61
0

Hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta NCDC a Najeriya ta ce ƙarin mutum 859 sun kamu da cutar korona ranar Litinin.

Haka nan cutar ta yi ajalin wasu mutum biyu a Litinin ɗin.

Jiha 14 ne suka fuskanci ƙaruwar a wannan karon, ciki har da Abuja babban birnin ƙasar. Su ne:

Lagos (555) Abuja (57) Rivers (44) Plateau (43) Edo (41) Ondo (34) Kwara (23)       Kano (18) Ogun (16) Enugu (11) Oyo (6) Delta (5) Bauchi (3) Bayelsa (3)

Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 238,420 ne suka harbu da cutar a Najeriya, sannan ta kashe mutum 3,024. Sai dai mutum 212,770 sun warke kuma an sallame su.