Home Labaru Fadar Shugaba Kasa Ta Ce Rashin Mutunci Ne ‘Yan APC Majalisa Su...

Fadar Shugaba Kasa Ta Ce Rashin Mutunci Ne ‘Yan APC Majalisa Su Amince Da Tirsasa Dokar Zabe

66
0

Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa zai yi wahalar gaske a ce ‘yan majalisun dokoki ɓangaren APC su goyi bayan tirsasa kafa dokar da Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙi sa wa hannu, saboda tilas su yi biyayya ga jam’iyyar su.

Kakakin Yaɗa Labarai na Buhari, Femi Adesina ne ya bayyana haka a ciki wata tattaunawa da gidan Talabijin na Channels ya yi da shi.

Adesina ya ce duk tantagaryar rashin mutuncin ‘yan majalisa na ɓangaren APC, ba su yi gangancin bijire wa Shugaba Buhari ba.

Jam’iyyar APC ce dai ke da mafi rinjayen mambobin Majalisar Tarayya da mafi rinjayen Sanatoci.

Ciki makon jiya ne Buhari ya sa ƙafa ya yi fatali da Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe na 2021, bayan da majalisa ta aika masa tun a ranar 29 Ga Nuwamba, domin ya sa hannu.

Sai dai kuma an haƙƙaƙe cewa gwamnonin Najeriya ne su ka ja ra’ayin sa har ya ƙi sanya wa dokar hannu, saboda batun zaɓen fidda-gwani da ƙudirin ya ce za a riƙa yin ‘yar rinƙe, maimakon wakilan jam’iyya su riƙa yi.