Home Home Babban Bankin Najeriya Ya Fara Wadata Kasar Da Sabuwar Naira

Babban Bankin Najeriya Ya Fara Wadata Kasar Da Sabuwar Naira

30
0
Babban bankin Nijeriya CBN, ya kaddamar da wani shiri da zai taimaka wajen gaggauta yaduwar sabbin kudin Nijeriya da aka sauya wa fasali, gabanin karewar wa’adin mako guda da ya yi saura.

Babban bankin Nijeriya CBN, ya kaddamar da wani shiri da zai taimaka wajen gaggauta yaduwar sabbin kudin Nijeriya da aka sauya wa fasali, gabanin karewar wa’adin mako guda da ya yi saura.

An dai samar da shirin ne, musamman don mazauna yankunan karkara da daidaikun al’ummar da ke da ka’idar abin da za su iya cirewa a duk rana.

A cikin wata sanarwa da babban bankin ya fitar, ya ce za a yi amfani da shirin wajen kara wayar da kan al’umma, game da karewar wa’adin daina amfani da tsofaffin takardun kudin.

Bankin CBN, ya ce shirin zai ba dillalan da ke da lasisin sauya wa kowane mutum guda kudin da ba su wuce Naira dubu 10 ba tare da biyan kudin kamasho ba.

Kafin samar da wannan shirin dai, tuni Majalisar Dattawa da wasu gwamnoni sun bukaci karin wa’adin daina amfani da tsofaffin kudin da aka sauya wa fasali.