
An soke dokar bayar da tazara da aka tilasta a Masallacin Ka’aba a Makkah da kuma na Annabi a Madina, kamar yadda hukumomin da ke kula da Masallatan Biyu Masu Daraja na Saudiyya wato Haramain Sharifain suka bayyana.
Hukumomin sun ce Matakin zai fara aiki ne daga ranar Lahadi, inda suka ce za a ci gaba da cika masallatan biyu kamar yadda aka saɓa kafin annobar korona.
Sun ce Wannan kuma na zuwa ne bayan ma’aikatar kula da harakokin cikin gida ta bayar da umarnin buɗe masallatan gaba ɗaya da kuma sasasauta matakan kariya da aka ɗauka.
Hakan na nufin za a bari mutane su gudanar da ibadah ba wani shamaki a wuraren Dawafi da Safa da Marwa a Masallacin Ka’aba.
Sai dai tun da farko hukumomin Saudiyya sun ce dole sai wanda ya kammala allurar rigakafin korona (guda biyu) kafin ya shiga masallacin Makkah da Madina, sannan har yanzu dokar sanya abin rufe baki da hanci na nan ga baƙi masu ibadah da kuma ma’aikatan da ke kula da masallatan.
You must log in to post a comment.