
Jakadan Najeriya na musamman a Yankin Tafkin Chadi Ambasada Babagana Kingibe, ya ce ana iya tattauna makomar Najeriya sakamakon barakar da ake samu daga yankuna daban daban wadanda ke bukatar sake fasalin yadda ake tafiyar da kasa.
Babagana Kingibe wanda ya yi jawabi a wajen bikin karrama shi da a kayi a birnin Lagos, ya ce ko da tsakanin mata da miji akan tattauna yadda zamantakewar su ke tafiya, saboda haka babu dalilin da za’a ce ba za’a iya tattauna makomar hadin kan Najeriya ba.
Sai dai tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayyar ya shaidawa masu bukatar raba Najeriya cewar, babu yadda za’a iya tsaga kasa da masu fafutukar raba Najeriya ke bukata koda kuwa an karkasa ta.
Kingibe ya bayyana cewar a Najeriya aka haife shi, kuma a Najeriya ya girma, kana shi da mutanen da suka yi rayuwa da na ci gaba da amincewa da dorewar kasar mu.
You must log in to post a comment.