Home Labaru Nijar Ta Kaddamar Da Kwalejin Hafsoshin Soji Ta Farko

Nijar Ta Kaddamar Da Kwalejin Hafsoshin Soji Ta Farko

26
0

Jamhuriyar Nijar dake fuskantar yawaitar hare-haren daga kungiyoyin ‘yan ta’adda, ta bude makarantar soji ta farko a Yamai babban birnin kasar domin horas da hafsoshin ta masu zuwa.

Da yake jawabi yayin bukin kaddamar da makarantar, Shugaba Mohamed Bazoum ya ce kasarsa, a matsayinta na makwabciyar Libya mai fama da tashin hankali, dole ne ta yi aiki kan bukatun tsaro duba da matsayinta a tsakiyar yankin da ke fuskantar ayyukan ta’addanci.

Ya ce cibiyar za ta zama muhimmiyar hanyar ƙarfafa tsaron ƙasar dake da iyakoki da Najeriya da Benin a kudunci, sai Burkina Faso da Mali a yamma, Algeria da Libya a arewaci sai kuma Chadi dake gabashin ta.

Rukunin farko zai kunshi jami’ai 26 da aka dauka daga sojoji, jandarma da masu tsaron kasa wadanda za su yi horo na watanni tara a karkashin malamai na kasa, in ji kwamandan makarantar Abdoul Razak Ben Ibrahim.