Home Labaru Zaɓen 2023: Masana Sun Bayyana Dalilan Da Suka Sa Wasu Gwamnonin APC...

Zaɓen 2023: Masana Sun Bayyana Dalilan Da Suka Sa Wasu Gwamnonin APC Ke Son Tsayar Da Jonathan Takara

243
0

Masana harkokin siyasa a Najeriya sun fara tofa albarkacin bakin su a kan rahotannin da ke cewa jam’iyyar APC mai mulki na zawarcin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan domin ya tsaya takara a karkashin inuwar jam’iyyar a babban  zaɓen 2023.

Wani rahoto dai yace wasu gwamononi daga arewa ne ke matsawa wajen ganin hakan ya tabbata, inda suka bayar da hujjar cewa saboda wa’adi ɗaya kawai tsohon shugaban ƙasar zai yi, sai mulki ya sake komowa yankin arewa.

To amma masana game da siyasar Najeriya na cewa hakan alama ce da ke nuna rashin aƙida a tsakanin ƴan siyasa masamman ‘ya’yan jam’iyyar APC.

A cewar masanan, wasu manyan jam’iyyar sun gwammace tsohon shugaban ƙasar ya kasance magajin shugaba Buhari, saboda ba zai musu bi-ta-dakulli ba, bayan haka ma zai fi daɗin tafiya a kan wanda zai fito daga wata shiyya ta daban, sannan kuma ba zai wuce wa’adi daya ba ganin cewa tun a baya ya yi wa’adi guda, bayan hakan sai mulki ya dawo ga ‘yan arewa.