Home Labaru Harkar Tsaro: Dalilin Da Ya Sa Tsofaffin Manyan Hafsoshin Tsaro Su Ka...

Harkar Tsaro: Dalilin Da Ya Sa Tsofaffin Manyan Hafsoshin Tsaro Su Ka Gaza – Wike

191
0

Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers, ya ce kalubalen tsaron da aka samu a karkashin jagorancin tsoffin hafsoshin tsaro sun wanzu ne saboda shiga siyasa da su ka yi.

Wike ya bayyana haka ne, yayin wata hira da ya yi a gidan talabijin na Channels, inda ya ce maimakon su maida hankali wajen tsaron Nijeriya, amma sai manyan hafsoshin su ka tsoma kan su a harkokin siyasa.

Ya ce Matsalar da aka samu da tsofaffin hafsoshin tsaron shi ne shiga siyasar da su ka yi maimakon maida hankali a kan tsaron Nijeriya.

Gwamna Wike, ya ce babu wanda zai musanta cewa, matukar aka sa siyasa a harkar tsaro to tabbas za a samu matsaloli, ya na mai cewa matukar sabbin hafsoshin tsaron da aka nada suka bi hanyar tsofaffin babu abinda za su iya yi.