Home Home Zaɓen 2023: Babu Wasu Sunayen Ƙarshe Na ‘Yan Takara Da Muka Fitar...

Zaɓen 2023: Babu Wasu Sunayen Ƙarshe Na ‘Yan Takara Da Muka Fitar – INEC

26
0
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kan Ta Ta Kasa Inec, Ta Ƙaryata Wasu Labarai Da Ke Yawo A Shafukan Sada Zumunta Cewa Ta Saki Sabbin Sunayen Ƙarshe Na ‘Yan Takara Gabanin Babban Zaɓen Shekara Ta 2023.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kan Ta Ta Kasa Inec, Ta Ƙaryata Wasu Labarai Da Ke Yawo A Shafukan Sada Zumunta Cewa Ta Saki Sabbin Sunayen Ƙarshe Na ‘Yan Takara Gabanin Babban Zaɓen Shekara Ta 2023.

A Wani Sako Da Hukumar Ta Fitar Ɗauke Da Sa-Hannun Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai Da Ilimantar Da Masu Jefa Ƙuri’a Festu Okoye, Ta Ce Babu Wasu Sabbin Sunayen ‘Yan Takara Da Ta Fitar Kamar Yadda Rahotonnin Ke Bayyanawa.

Hukumar Zaben Ta Yi Kira Ga Jama’a Su Yi Watsi Da Labarin,  Domin A Cewar Ta, Ta Kan Fitar Da Sunayen Ƙarshe Na ‘Yan Takara Kwanaki 150 Kafin Ranar Zaɓe, Kamar Yadda Sashe Na 32 (1) Na Dokar Zaɓe Ta Shekara Ta 2022 Ta Tanada.

Sanarwar Ta Kara Da Cewa, Tuni Hukumar Ta Fitar Da Sunayen Ƙarshe Na ‘Yan Takarar Shugaban Ƙasa Tun Ranar 20 Ga Watan Satumba, Yayin Da Ta Fitar Da Na ‘Yan Takarar Gwamna A Ranar 4 Ga Watan Oktoba.