Home Labaru Yunwa Ta Sa Wadanda Aka Yi Garkuwa Da Su Cin Ciyawa A...

Yunwa Ta Sa Wadanda Aka Yi Garkuwa Da Su Cin Ciyawa A Jihar Zamfara

47
0

Wasu daga cikin mutanen da jami’an tsaro su ka kubutar daga hannun ‘yan bindiga a Jihar Zamfara, sun bayyana yadda su ka kwashe kwanaki 53 su na cin ciyawa saboda rashin abinci domin tsira da rayukan su.

Wadanda su ka tsira da rayukan su, sun ce akalla 17 daga cikin su sun mutu a dajin da ake tsare da su, yayin da su kuma su ka sha da kyar saboda rashin abinci kafin a kubutar da su.

Sakamakon matakan da gwamnati da jami’an tsaro su ka dauka dai, ‘yan bindiga su na fuskantar wahala wajen ciyar da mutanen da su ke garkuwa da su.

Sakataren gwamnatin Jihar Zamfara Kabiru Balarabe, ya ce yanzu haka jami’an kula da lafiya su na kula da mutane kusan 200 da aka ceto domin duba lafiyar su da kuma taimaka masu.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Ayuba Elkana, ya ce sakamakon matsin lamba da kuma rashin abinci, yanzu haka ‘yan bindiga su na shan wahala wajen gudanar da harkokin su a jihar.