Home Labaru Kasuwanci Ya Zama Kamfani Mafi Girman Hannun Jari A Nijeriya

Ya Zama Kamfani Mafi Girman Hannun Jari A Nijeriya

14
0

Hukumar kula da harkokin Kamfanoni da kasuwanci ta Nijeriya CAC, ta ce kamfanin man fetur na ƙasa NNPC ya kafa tarihi, yayin da hannun jarin sa ya zarce na kowane kamfani a Nijeriya.

Magatakardan hukumar Garba Abubakar ya bayyana haka a Abuja, yayin da ya ke gabatar wa Shugaba Buhari rajistar sauya fasalin kamfanin a fadar shugaban ƙasa.

Kamfanin dallancin labarai na Nijeriya NAN, ya ruwaito Shugaba Buhari ya na bayyana jin daɗin sa game da nasarar da NNPC ya samu.

Abubakar, ya ce an yi wa kamfanin rajista cikin kwana ɗaya ta Yanar Gizo, wanda darajar hannun jarin sa a tashin farko ta kai naira biliyan 200 tun ranar 22 ga watan Satumba.