Home Labaru Mayakan Sa-Kai Sun Kashe Mutane 11 A Jihar Sokoto Ciki Har Da...

Mayakan Sa-Kai Sun Kashe Mutane 11 A Jihar Sokoto Ciki Har Da Limami

11
0

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan wata kungiyar yan sa-kai ne a jihar Sokoto, sun kashe mutane 11, ciki har da wani Limami a kauyen Mamande da ke karamar hukumar Gwadabawa.

Rahotanni sun ce, wadanda lamarin ya rutsa da su sun mutu nan take, yayin da wasu mutane hudu da su ka samu raunin harbin bindiga aka garzaya da su asibiti domin yi masu magani.

Limamin mai suna Malam Aliyu, wata majiya ta ce ya na jagorantar sallah ne a lokacin da ‘yan bindigar su ka afka masu.

Bayanai sun ce wadanda abin ya rutsa da su sun fito ne daga garuruwan Fulani daban-daban da ke kusa da yankin domin sayen abinci da sauran kayayyaki a kasuwar Mamande ta mako-mako.