Home Labaru Ilimi Yunkurin Yi Wa Kungiyar ASUU Kishiya Ya Kankama A Jami’o’i

Yunkurin Yi Wa Kungiyar ASUU Kishiya Ya Kankama A Jami’o’i

458
0
Kungiyar Malaman Jami’o’i Ta Nijeriya ASUU
Kungiyar Malaman Jami’o’i Ta Nijeriya ASUU
Chris Ngige, Ministan kwadago Da Samar Da Ayyuka
Chris Ngige, Ministan kwadago Da Samar Da Ayyuka

Ministan Kwadago Chris Ngige ya tabbatar da cewa, wata kungiyar malaman jami’o’i mai suna ‘CONUA’, ta mika takardar neman amincewar mallakar rajistar zama kungiya a ofishin sa.

Wadanda su ka kafa kungiyar dai sun balle ne daga Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya ASUU.

Ngige, ya ce tun cikin watan Afrilu masu neman kafa kungiyar su ka kai takardar a ma’aikatar sa, amma ba a kai ga yi mata rajista ba.

Sabuwar kungiyar dai ta fara bayyana ne daga Jami’ar Obafemi Awolowo, kuma tuni ta fara samun goyon baya daga wasu jami’o’i.Jami’in sabuwar kungiyar Niyi Ismaheel, ya ce sun yi tunanin kafa kungiyar ne don a samu zaman lafiya a jami’o’in Nijeriya, domin a cewar sa, yawan tafiya yajin aiki da ake yi ya na gurgunta karatu, kuma ya na kawo jinkirin shekara da shekaru ga dalibai kafin su kammala digiri.

Leave a Reply