Home Labaru Mulki Ya Nuna Wa Kowa Ainihin Fuskar Shugaba Buhari – Buba Galadima

Mulki Ya Nuna Wa Kowa Ainihin Fuskar Shugaba Buhari – Buba Galadima

317
0

Tsohon na hannun damar shugaba Buhari Injiniya Buba Galadima, ya ce mulki ya tona wa shugaba Muhammadu Buhari asiri, lamarin da ya bayyana a matsayin abin kunya.

Buba Galadima ya bayyana haka ne, yayin wata hira da Jaridar New Telegraph ta yi da shi, inda ya ce da Buhari ya tsaya a kan manufofin da aka san shi da su a baya, da tuni Nijeriya ta cigaba a mulkin sa.

Ya ce Buhari ya samu abin da ya ke so na mulkin Nijeriya ne bayan ya hada kai da sauran bangarorin kasar nan, sai dai bayan ya samu mulkin ne halayyar sa ta gaskiya ta bayyana.

Galadima, ya ce shugaba Buhari ya san abin da ya kai ga kujerar mulki, kuma ya san irin sadaukarwar da wasun su su ka yi don ganin ya zama shugaban kasa, amma ya na samun mulki ya fatattake su. Ya ce an yi watsi da duk wadanda su ka yi wa shugaba Buhari gwagwarmaya, har ta kai ga an tsare wasu da sunan sun ci amanar kasa.