Home Labaru An Karfafa Tsaro Yayin Da Kotu Ke Zaman Raba Gardamar Zaben Gwamna

An Karfafa Tsaro Yayin Da Kotu Ke Zaman Raba Gardamar Zaben Gwamna

233
0

Rahotanni daga jihar Bauchi na cewa, an karfafa tsaro ciki da wajen kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar, yayin da Alkalan kotun ke zaman raba gardama tsakanin gwamnan jihar Bala Mohammad na jam’iyyar PDP da Mohammed Abubakar na jam’iyyar APC.

Jami’an tsaro da su ka hada da ‘yan sanda da jami’an tsaro na farin kaya Civil Deffence, da na hukumar tsaro ta DSS da wasu na leken asiri sun mamaye titunan Ahmadu Bello da ‘Yandoka da safiyar Litinin din nan.

An dai kulle hanyar gaba daya, an kuma umurci mutane su bi wasu hanyoyin daban, lamarin da janyo matsala ga masu motocin haya da yan kasuwa da ofisoshin ma’aikatan gwamnati da aka kulle, yayin da jami’an tsaro su ka hana mutane shiga harabar kotun, ciki kuwa har da manema labarai.

Tsohon gwamnan jihar Bauchi dai ya sha alwashin maka gwamnatin Jihar Bauchi kotu, bisa rahoton da wani kwamitin gwamnati ya fitar cewa ana zargin sa da baddakalar wasu kudade.