Home Labaru Kiwon Lafiya Yunkurin Tserewar Fursononi: Labarin Kanzon Kurege Ne- Sanusi Dan Musa,

Yunkurin Tserewar Fursononi: Labarin Kanzon Kurege Ne- Sanusi Dan Musa,

419
0

c, ya kwatanta rahoton da wasu kafofin yada labarai ke yadawa da labarun kanzon-kurege, wadanda ba gaskiya a cikinsu.

Shugaban hukumar gidajen gyaran hali na jihar Kaduna, Sanusi Mu’azu Danmusa

Ya bayyana hakan ne a matsayin martani akan rahoton balle gidan gyaran hali na Kaduna da mazauna gidan suka yi yunkurin aikatawa.

Danmusa, ya ce tabbas wasu daga cikin mazauna gidan sun yi yunkurin balle gidan a ranar 31 ga watan Maris din shekarar 2020.

Shugaban ya bayyana cewa tuni hukumar gidan ta yi bayani a kan aukuwar lamarin amma duk haka ta kara yanke shawarar kara bayani ne don mayar da martani a kan rade-radin da ke yawo a gari.

Ya kara da cewa, “an fara gudanar da bincike kamar yadda shugaban hukumar kula da gidajen gyaran hali na Najeriya, Alhaji Jafaru Ahmed, ya bada umarni.