Home Labaru Kiwon Lafiya Gwajin Covid-19: – Gwamna Makinde Ya Warke Daga Cutar

Gwajin Covid-19: – Gwamna Makinde Ya Warke Daga Cutar

374
0

Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde, na jam’iyyar PDP, ya ce sakamakon gwajinsa na biyu ya sake nuna cewa yanzu ba ya dauke da kwayar cutar covid-19.

Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde

Gwamna Makinde,  ya sanar da hakan ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, inda ya mika godiyarsa ta musamman ga mutanen jihar sa bisa damuwar da suka nuna a kansa tare da yi masa addu’o’in samun lafiya.

A ranar Litinin, 30 ga watan Maris, ne gwamna Makinde ya sanar da cewa sakamakon gwajin da aka yi masa ya nuna cewa yana dauke da kwayar cutar covid-19.