Wasu rahotanni sun tabbatar da mutuwar wani kasurgumin dan bindiga mai garkuwa da mutane a jahar Katsina mai suna Abdulhadi Dan Nashe.
Rahotannin sun bayyana cewa Dan-Nashe ya gamu da ajalinsa ne a hannun yaransa bayan sun yi masa bore, sun juya masa baya sakamakon wata rashin fahimta da aka samu a tsakanin su.
Rashin fahimta da ya kunno kai a tsakanin ‘yan-bindigan baya rasa nasaba da wata tirka-tirka da ta taso tsakanin Dan-Nashe da matarsa, wanda ita kan kanwa ce ga wani shugaban yan bindiga, mai suna Dangote.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan-bindiga dake biyayya ga Dangote ne suka kai samame gidan Dan-Nashe, inda suka kashe shi.
Shi dai Dan-Nashe ya yi kaurin suna wajen satar mutane, shirya hare hare da kuma ciniki da fataucin miyagun makamai.
You must log in to post a comment.