Home Labaru Yawan ‘Yan Kasa: Za A Yi Kidayar ’Yan Nijeriya Cikin Watan Yuni...

Yawan ‘Yan Kasa: Za A Yi Kidayar ’Yan Nijeriya Cikin Watan Yuni Na Shekara Ta 2021 — NPC

181
0

Shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa, NPC, Nasir Issa Kwarra, ya ce hukumar ta shirya gudanar da aikin kidayar ’yan Nijeriya cikin watan Yuni na shekara ta 2021.

Ya ce aikin kidayar zai fara ne daga tsakiyar shekara ta 2021 zuwa farkon shekara ta 2022.

Kwarra ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai, inda ya bayyana irin ci-gaban da hukumar ta samu a karkashin sa, dangane da shirye-shiryen fara aikin gudanar da kidayar.

Nasir Issa Kwarra , ya ce ya na sane da yadda aka samu tsaikon fara aikin kidayar har tsawon shekaru biyar, sai dai ya ce duk wannan lokacin hukumar ta na tuntubar gwamnatin tarayya don a bada umarni.

Ya ce tuni hukumar ta fara aikin tantancewa da rarrabe kan iyakokin tsarin kidaya na yankuna da garuruwa da jihohi.