Home Labaru Wariya: Masu Fama Da Nakasa Sun Yi Zanga-Zangar Lumana A Jihar Adamawa

Wariya: Masu Fama Da Nakasa Sun Yi Zanga-Zangar Lumana A Jihar Adamawa

143
0

Hadakar kungiyoyin nakasassu a jihar Adamawa, sun gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna fushin su bisa zargin cewa ba a kulawa da su musamman a wannan lokaci na annobar COVID-19 da matsin tattalin arziki da tabarbarewar tsaro.

Nakasassun sun yi zanga-zangar ne har zuwa gidan gwamnatin jihar, inda jami’an gwamnatin su ka tarbe su.

Da su ke gabatar da koken su a gaban gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri, wanda babban hafsa a gidan gwamnatin jihar Farfesa Maxwell Gidado ya wakita, nakasassun sun koka game da abin da su ka kira rashin kula da bukatun su.

Daya daga cikin shugabannin kungiyar, ya ce ba su je gidan gwamnati da niyar yin zanga-zanga ba, amma su na jan hankalin mahukunta su dubi halin da suke ciki, su kuma tuna da irin goyon bayan da su ka ba gwamnan a lokacin yakin neman zabe.

Shugaban kungiyar nakasassu na Mubi Aliyu Muhammad Abubakar, ya ce akwai masu karatu a cikin su, amma abin takaici shi ne ba a ba su aiki kuma ba a ba su hakkokin su na tallafin kyautata rayuwa.